Friday 28 February 2020

CASHLESS - A TAKAICE


22/09/2019

CASHLESS - A TAKAICE

Cashless Policy - Wata doka ce da aka kirkiro domin a takaita mu'amala da tsuran kudi a wajen hada-hada da ciniki tsakanin jama'a ko masana'antu da sauransu. Ta yanda za'a karfafa amfani da hanyoyin cinikayya na zamani kamar ta hanyar amfani da ATM, ko POS, ko ta yanar gizo wato internet banking ko web purchase, ko kuma ta hanyar amfani da waya (code/app) wato mobile banking. Wannan shiri ko doka ta CASHLESS an kirkiro shi a Najeriya a shekarar 2011, lokacin ance zata fara aiki ne a garin Legas a 20th March, 2012. Sannan a July 1, 2013 a fadadata zuwa garuruwan Abia, Anambra, Rivers, Ogun, Kano da kuma Abuja. Hakanan za'a ida fadadata zuwa ko ina a kasar a shekarar 2015. A wancan lokacin an sanya cewa duk mutumin da zai sanya ko fitar da kudin da suka wuce N150,000 to duk abinda ya hau za'a caji mutum 10% na abinda ya hau akan N150,000. Hakanan suma masana'antu duk kudin da zasu fitar ko sanyawa da suka wuce N1,000,000 to duk abinda ya hau za'a caje shi 20%.

Daga baya kuma sai bankin na CBN ya sake nazari akan cajin da kuma iya kudin da in suka wuce za'a caji mutum, inda aka maida shi cewa maimakon N150,000 a da to yanxu mutum zai iya sanyawa ko cire N500,000 kullum a kyauta, amman da zaran kudin sun wuce to zai biya caji, inda shima cajin da za'a yiwa mutum in zaisa kudi maimako 10% aka dawo dashi 2%, wajen cirewa ma maimakon 10% ya dawo 3%. Suma masana'antu da aka sake nazarin dokar sai aka ce a maimakon huddar N1,000,000 da zasu iyayi ba tare da wani sabon caji ba an maida shi zuwa N3,000,000. Sannan idan zasu cire kudi za'a caje su 5% akan kudin da suka hau maimakon 20% a da, sannan idan zasu sa kudi za'a caje su 3% akan kudin da suka hau maimakon 20% a da.


JADDADA DOKAR
A can baya dai dokar batai tasiri ba sosai amman yanzu babban bankin na Najeria ya sake jad dada dokar kamar yanda aka sake nazarinta a baya wato:

1- Idan mutum zaiyi hada-hadar N500,000 ko kasa da haka a yini to ba wani sabon caji idan kuma suka wuce to za'a caji 3% in fiddowa ne ko 2% in sakawa ne.

2- Sai masana'antu suma zasu iya hada-hadar N3,000,000 ko kasa da haka to ba wan sabon caji amman idan suka wuce haka za'a caje su 5% idan fiddawa ne idan kuma sanyawa ne 3%.

3- Dokar ta shafi hada-hadar tsuran kudi ne, amman banda transfer.

4- Hakanan ko cheque wani ya baka ko kaba wani akwai iya kudin da banki zai iya ya baka ba tare da an caji kudi ba.

Cajin ana yinsa ne akan kudin da suka wuce iyakar da aka fidda. Misali: idan mutum ya cire ko sanya N500,000 ko kasa da haka to kyauta ne, ba karin caji amman idan misali N520,000 ne to wannan doriyar N20,000 data hau ita kadai za'a yiwa cajin, alal misali idan cirewa ne N20,000 ta hau (3%) za'a caji mutum N600 kenan idan kuma sanyawa ne N20,000 ta hau (2%) za'a caji mutum N400 kenan.

Yanzu dokar za'a fara aiwatar da ita ne a ranar 18th September, 2019 a garuruwan Lagos, Abia, Anambra, Rivers, Ogun, Kano da kuma Abuja. Sannan za'a fadadata zuwa ko wace jiha a ranar 31st March, 2020.


AMFANIN DOKAR
1- Zata taimaka wajen raguwar fashi da makami da sauran hadurran rike kudi zabarsu.

2- Gwamnati zata kara samun kudin shiga, kuma zata rage kashe kudi wajen buga sabbin kudade.

3- Bankuna da Masana'antu zasu rage kashe kudin da suke wajen dawainiya da tsabar kudade.

4- Zai taimaka wajen gano masu halatta kudin haram da kuma sa'ido kan ayyukan yan ta'adda.


KALUBALE
1- Rashin ilimi musamman abinda ya shafi amfani da na'urorin zamani.

2- Rashin wutar lantarki da kuma network ingantacce da za'a iya dogaro akai.

3- Rashin wadatattun na'urori kamar su ATM da POS.

4-  Rashin cikakken tsaro a wuraren da keda na'urorin fitar da kudi, saboda za'a iya yiwa mutum kwace ko fashi.

5- Akwai yiwuwar damfarar mutane musamman wadanda basu san ya zasu yi amfani da na'urorin zamani ba.


KORAFI
1- Jama'a na korafi ne akan cewa akwai yiwuwa kara yawan cajin da akewa mutane idan sunyi sayayya ta hanyar biyan kudin da ATM, POS, Mobile banking da Internet banking ko Web purchases.

2- Mutane na ganin cewa idan ana son jama'a su karbi shirin sosai to akwai bukatar a rage cajin ko kuma ma ya zamana cewa akwai wata garabasa ta musamman ga wadanda suka rungumi tsarin sauda kafa.

3- Wasu mutanen kuma na ganin dokar bata dace ba a yanzu ganin halin tattalin arziki da jama'a da masana'antu ke ciki.


©Mus'ab Nuraddeen Katsina (Mus'abulkhair)
E-mail: musabnurakatsina@gmail.com
Twitter/Instagram: @Musabulkhair_kt





Tuesday 2 January 2018

ALMAJIRCI DA BARA A MAHANGAR ILIMI



ALMAJIRCI DA BARA A MAHANGAR ILIMI: WAIWAYE A KAN YIWUWAR HANI KO CIGABAN AIWATAR DA SU





                                                                                     DAGA







                                                                     MUSAB NURA KATSINA                                                                                                                                             (MUS'ABULKHAIR)
                                                        musabnurakatsina@gmail.com
                                                                               07069530325
















                                                                     JANAIRU, 2017









Gabatarwa

Assalamu Alaikum Warahtullahi Wabarakatuhu
Ya yanuwa masu daraja, manufar wannan takarda ita ce a jefi tsuntsu biyu da dutse xaya. Wato a shimfixa tabarmar nazari dangane da wasu muhimman matsaloli guda biyu da suka daxe suna ci wa alumma tuwo a qwarya, wato Almajirci da bara tare da qoqarin tantance matsayin kowane a cikinsu. Domin kuwa masana da dama da hukumomi da sauran manazarta sun yi wa wannan batu kallon garau a mahangar addinin Musulunci, sannan suka ayyana raayoyi mafi dacewa fiye da shurin masaqi.  A xaya vangare kuma, takardar za ta yi qoqarin lalubo bakin zaren wasu dalilan da suka sa ximbin alumma ba su fahimci mene ne haqiqanin abin da ake nufi da waxannan matsaloli ba.
Ina fatan alumma za su nazarci wannan taqaitacciyar muqala a cikin kyakykyawar fahimta, tare da qoqarin bayar da gudummawar hanyoyin da za a havvaka ta don ganin an cim ma gaci. Saboda haka akwai matuqar muhimmanci a fahimci maanar muhimman kalmomi guda biyu, wato Bara da Almajirci.

1.1 Bara
 Kalmar bara tana nufin neman taimako kamar abin daya shafi abinci, kayan sawa (sutura), kuxi da sauransu, musamman ga waxanda suka tagayyara a sakamakon abkuwar wata musiba data same su.  Wasu daga cikin waxannan nauoin musiba sun haxa da; rashin wadata, rashin lafiya, haxari, karayar arziki, kora daga aiki, ambaliyar ruwa da sauran makamantansu.

1.2 Almajirci
Kalmar almajirci ta samo asali ne daga harshen Larabci, wato Almuhajir kafin daga bisan harshen Hausa da Bahaushe suka mai da ta Almajiri.  Bisa ma’ana kuwa, ita kalmar almuhajir a larabci tana nufin wanda ya yi qaura ya bar garinsu domin ya kuvuta da addininsa da mutuncinsa kamar yadda Musulman farko suka yi. Har wa yau kuma, ta haka ne shi kuma Bahaushe ya faxaxa maanar kalmar inda yake kiran duk wani wanda ya bar garinsu zuwa wani gari domin neman ilimin addininsa da sunan Almajiri.


2.0 Almajirci A Wajen Alumma
A zamani mai tsawo da ya shuxe, alummu sun riqa taimaka wa bayin Allah musamman almajirai da nauoin abubuwa da dama da suke iyawa kamar abinci da sutura.  A wasu lokutta kuma har sukan haxa da ‘yan kuxi domin su ji daxin neman ilimin da suka zo nema, musamman a Masallatai inda mafi yawa a nan suke yada zango. To, ganin irin wannan taimako da alumma suke ba almajirai, ya sa wasu masu matattar zuciya da lalaci suka ari rigar almajirai suka yafa, wato suka riqa zuwa masallatai da gidaje da wuraren taruwar jamaa suna barar a taimaka masu da sunan su ma wai almajirai ne. Ta haka ne kuma aka riqa samun mutane suna shiga rigar malanta, su karvo yara daga qauye da sunan za su karantar da su amma sai su riqa yawo da su gari-gari don yin bara.  Bisa yawanci, idan suka sauka a baqon gari shi malamin zai samar wa kansa masauki, su kuwa sauran yaran sai kowa ya je ya nemi wurin kwana da abinda zai ci.  A wasu lokutta kuwa, su yaran ne za su tanadar wa malamin abin da zai ci.

Mafi yawan iyaye suna ba malamai masu yawo ‘yayansu ne domin su karantar da su, saboda sun yi imani cewa yaransu za su sami ingantaccen karatu.  Domin waxannan bara-gurbin malaman sun riga sun kwaxaitar da su cewa yin bara da yawo shike sa a sami ingantaccen karatu. Sai dai kuma abin da ke faruwa a qarshe shi ne wasu daga cikin yaran sukan bijire wa malamansu, har ma su shiga birane su yi zamansu, ba tare da yin laakarin irin aikin da waxannan yara suke aiwatarwa ba, wato mai kyau ko akasin haka.  Domin kuwa za ka ga wasu suna dako, ko yin aikatau, wasu kuma har sukan zama masu aikin matan bariki. Idan tafiya ta yi tafiya, wato yaro ya saba da riqe kuxi da jin daxin zuwa gidajen kallo da sauran halayen jin daxin rayuwa na birni sai ka ga ya tashi a tutar babu, wato shi bai sami karatun ba kuma bai koma gida da zama ba.
Wasu iyayen kuwa suna tura ‘yayansu almajirci ne saboda suna hasashen idan yaran suna can makarantar, to sun huta da duk wata nauin xawainiyarsu ta abinci da sutura har ma kula da lafiyarsu.  Domin kuwa da wahala ka ga mahaifin yaro ya yarda cewa bara yaje garin da yaronsa yake karatu ya ga halin yake ciki, ballantana a ce ya riqo wani abin da ya shafi abinci ko sutura ya kawo masa yadda zai sami qwarin-gwiwar ci gaba da karatunsa.  Hasali ma, sai ka ga iyayen ne suke jira idan yaran za su zo ganin gida su taho masu da wani abu, wanda hakan ke nuna cewa wasu iyayen ma suna ganin zuwa almajirci kamar zuwa cirani ne ba neman ilimi ba.
Idan muka lura da bayanin daya gabata a sama da kyau za mu ga cewa almajirci ba shi ke haifar da yin bara ba, kuma za a iya yin almajirci ba tare da an yi bara ba. Sai dai kuma yin hakan ba zai yi tasiri ba sai an xauki wasu muhimman matakai da za su taimaka don ganin an fitar da jakai daga duma.

3.0 Bara A Mahangar Musulunci
A zahirin gaskiya addinin Musulunci ba ya goyon bayan yin bara ko kaxan, hasali ma har kullum Musulunci yana qarfafa mana gwuiwa ne mu dage da yin wani aiki ko wata sanaar da za mu dogara da ita har ma mu taimaka wa wasu. Domin yin roqo yana jawo wa mai yin sa qasqanci da wulaqanci da rashin qima a idanun mutane. Manzon Allah tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya yi gargaxi game da yin bara a cikin Hadisai da dama. Imam Bukhari da Imam Muslim Allah ya yarda da su sun ruwaito Hadisi daga Abdullahi xan Umar Allah ya qara masu yarda cewa, Manzon Allah tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya ce, Mutum ba zai dage yana ta yin bara ba har sai ya zo a ranar alqiyama da fuskarsa ta ziganye ba tsoka ko kaxan a jikinta”.
Haka nan kuma Imam Bukhari Allah ya yarda da shi ya ruwaito hadisi daga Abu Huraira Allah ya yarda da shi cewa, Manzon Allah tsira da amincin Allah su kara tabbata a gareshi ya ce, Na rantse da wanda rayuwata ke hannunsa, ya fi wa mutum kyau ya je yawo ita ce ya zo ya saida da a ce ya je ya tambayi wani abu a wurin wani. Domin kuwa zai iya ba shi kuma zai iya hana shi”.
Mutane uku ne kaxai addinin Musulunci ya yarda su yi bara.  Ga su kamar haka:

i- Mutumin da ake bi bashi kuma lokacin biyan bashin ya yi bai da halin biyan kuxin, to shi zai iya yin bara domin ya samu ya biya waxannan kuxin, kuma idan ya samu ya biya to bara ta haramta a gare shi.

ii- Sai mutumin da wata masiba ta same shi ko ta sami dukiyarsa.  Shi ma zai iya yin bara har ya sami xan abin da zai gudanar da rayuwarsa, shi ma daga nan bai kamata ya ci gaba da yin bara ba.

iii- Sai kuma mutumin da talauci ya yi wa katutu har aqalla mutane ukku suka tabbatar da hakan.  To, shi ma ya halatta ya yi bara har ya sami xan abin da zai riqe kansa daga nan shi ma bara ta haramta a gare shi.
A tsari na Musulunci ma bai kamata a ce ga wani ya shiga halin yunwa ko talauci har ta kai shi ga yin bara ba. Domin alhakin alumma ne su riqa taimakon junansu, musamman idan sun shiga wani hali na quncin rayuwa irin wannan ba tare da an bari ya faxa halin da sai ya yi bara ba.

3.1 Dalilan da ke Haifar da Bara
Ko shakka babu, akwai ximbin dalilai masu qarfi da suke haifar da yin bara a zamantakewar alumma.  Kaxan daga ciki sun haxa da:
i- Rashin gudanar da adalci daga masu shugabantar alumma, ta hanyar wadatar da su da muhimman abubuwan more rayuwa a birane da karkara. Domin kuwa da a ce ana aiwatar da wasu muhimman ayyuka kamar samar da wuta da ruwa da ilimi da kiwon lafiya a qauyuka, to da an qara samun sauqin masu aiwatar da bara saboda mutane ba za su rasa abin yi ko da a qauyuka ne ba.
ii- Lalacewar zumunci, inda za ka ga jamaa ba su taimakon ‘yanuwansu da masu buqatar hakan.
iii- Mutuwar zuciya, ta yadda za ka ga mutum da lafiyarsa da qarfinsa, amma ya gwammace ya yi bara a kan ya je ya nemi sanaa.
iv- Rashin taimakon waxanda suka tagayyara a sakamakon wata musifa ko balai da ya fada masu.  Misali,
Rashin lafiya
Haxari
Karayar arziki
Ambaliyar ruwa
Tsufa. Da sauran makamantansu.

3.2 Rabe-Raben Mabarata
Mabarata a zamantakewar alumma sun kasu zuwa manyan gidaje guda biyu kamar haka:
Musakai
Wannan aji na mabarata ya qunshi alumma da dama da suka haxa da:
i- Guragu
ii- Kutare
iii- Makafi
iv- Kurame.
 Da dai sauran makamantansu.

Waxanda ba Musakai ba
Kamar aji na farko, shi ma wannan aji na biyu ya qunshi rukunin waxannan mutane kamar haka:
i- Yara almajirai.
ii- Tsafaffi waxanda danginsu/yanuwansu suka yi fatali da kulawarsu ba.
iii- Mahaukata.
iv- Akwai masu bara saboda camfi, kamar mata masu ‘yanbiyu.
v- Akwai kuma masu bara saboda lalaci da mutuwar zuciya.
vi- Haka nan kuma, akwai masu bara ta wani xan lokaci saboda wata musifa ko lalura da ta same su.

3.3 Illolin Bara
Bara dai tana da illoli kamar haka:
i- Bara tana jawo qasanci ga mai yin ta, har ma da alummar da masu yin ta  suka fito kamar dai yadda muke gani a yau.
ii- Tana jawo rashin ci gaba ko kuma koma bayan tattalin arzikin alumma. Domin masu yin bara za ka ga ba su bayar da gudummuwa ta hanyar yin wani aiki kamar leburanci, ko sarrafa wani abu, ko sayar da wani abu wanda zai taimaka wajen inganta tattalin arziki da rayuwar alumma.  Bisa yawanci, sai dai kawai kullum a ba su suka sani domin da wahala ka ga wanda ke bara a ce yana da gurin ya tara xan wani abu domin ya yi wata sanaa, sai dai kawai ya mai da barar ita ce sanaarsa.
iii- Har way au kuma, ya tabbata a addinance cewa bai kamata mutum ya yi bara ba, musamman idan ba a cikin wani mawuyacin hali ya sami kansa ba kamar yadda muka gani a sama.

3.4 Matakan da ya Kamata a bi Domin Magance Bara
Matakai ko kuma hanyoyin da ya kamata a bi domin a shawo kan matsalar bara sun kasu zuwa gida biyu:

Mataki Na Daya
i- Kafin a ce za a taimaki mabarata dole ne a tantace yawansu.
ii- A san sunayensu da inda suka fito domin a mai da su garuruwansu idan ba a ciki suke zaune ba.
iii- A san adadin kutareda makafi da guragu da kurame da sauransu.
iv- A san nawa ne adadin manya da na yara.
v- A san nawa ne za su iya koyon sanaa, kuma nawa ne ba za su iya koyon sanaa ba.
vi- Nawa ne suke da iyali (mata/yaya), kuma nawa ne ba su da iyali.
vii- Masu iyali yaya za a yi da iyalansu (mata/yaya).
viii- Mutum nawa ne suke da gatan da ‘yanuwansu za su kula da su, kuma nawa ne ba su da wannan gatan.

Mataki Na Biyu
i- Da farko dai kafin a hana musakai bara dole ne a fara hana masu lafiya.

ii- Musakan da suke yara ne, ya kamata a buxe masu makarantunsu su kaxai saboda gudun tsangwama idan an haxa su da waxanda ba musakai ba. A qalla makaranta guda a kowace qaramar hukuma. Domin suma su samu ilimin zamani.

iii- Ya kamata a hana kai yara qanana almajirci a makarantun da suka yi nisa da inda iyayensu suke zaune, matuqar yaran ba za su iya kula da kawunansu ba. Haka kuma ya kamata ya yi hukuma da masu hannu da shuni su riqa xaukar malamai waxanda za su iya zaunawa a karkara domin su riqa karantar da yara, sai a riqa biyansu albashi mai tsoka yadda zai ishe su biyan buqatunsu na yau da kullum daidai gwargwado.  Su kuma waxanda suke zaune a birane, ya kamata a riqa tallafa masu da taimaka wa yaran da abubuwan da suka kamata kamar abinci da ruwan sha, kamar ta hanyar gina rijiyar zamani yadda za su riqa amfani da ruwan wajen sha da sauran ayyukan tsaftace kansu da muhallinsu da kiwon lafiya. Domin idan aka ce za a xauki nauyin yaran da malamansu gaba xaya, to gaskiya aikin ba qarami ba ne kuma wasu iyayen da sun ga ana yi wa yaransu komai, to sai ka ga suna qara turo yaran ba dan karatun ba kawai, sai kawai don su huta da xawainiyar da suke yi masu.  Wannan kuma ba qaramin cikas zai kawo wa wannan shiri ba.

iv- Manyan mutane da ke bara saboda lalaci da mutuwar zuciya, ya kamata a hana su su je su nemi sanaa.

v- Manyan da ke iya koyon wata sanaa sai a kafa masu wuraren koyon sanaoi a kowace qaramar hukuma, inda za a riqa koyar da su sanaoi kala-kala. Kuma idan sun gama koyon sanaar, sai a ba su jari mai qwarin gaske ba wanda zai sa daga baya su sake komawa barar ba.

vi- Su kuwa tsofaffi da manyan da ba su iya koyon wata sanaa, sai a tanadar masu da gidajen jinqai na gajiyayyu inda za a riqa taimaka masu da abinci, sutura (kayan sawa), da kiwon lafiya. Idan kuma mutum yana da gatan da ‘yanuwansa za su iya kula da shi, sai a bar shi a wajen danginsa su kula da shi, ita kuwa hukuma sai ta riqa ba da tallafin ga danginsa na abin da za a riqa kula da shi.

vii- Gwamnati da hukumomin kiwon lafiya ya kamata su ma su qara himma wajen wadatar da magungunan cututtuka irin su kuturta da makanta, musamman a qauyuka inda nan ne cututtukan suka fi yawa da kuma saurin yaxuwa.

viii- Musakai waxanda ba su bara kuwa, ya kamata a haxa da su wajen bayar da duk wani nauin taimakon da aka shirya wa musakan da ke bara.  Domin fidda su a cikin tsarin zai iya sawa su ce an mai da su saniyar ware.
Musakan da ke xauke da cutar da za ta iya yaxuwa kamar kuturta dole a samar masu da matsugunninsu su kaxai, wato kada a haxa su da waxanda ba kutare ba don gudun yaxuwar cutar.

4.0 Hanyoyin da ya Kamata a bi Wajen Aiwatar da Wannan Shiri
Don ganin an aiwatar da wannan shiri da aka ambata a cikin nasara, akwai buqatar muhimman abubuwa guda biyu ne kamar haka:

4.1 Kuxi
Idan muka lura sosai za mu ga cewa, wannan shiri wani gagrumin shiri ne da ke buqatar kuxi masu yawan gaske domin aiwatar da shi.  Don haka, ya zama tilas a san ta waxanne hanyoyi ne za a iya samun isassun kuxin da za a aiwatar da wannan shiri.  Domin kuwa gwamnati ita kaxai ba za ta iya aiwatar da shirin yadda ya kamata ba, wato dole sai alumma ta tallafa kuma ta nuna kishinta da cikakken goyon baya domin a cim ma gaci. Saboda haka, wasu daga cikin hanyoyin da za a bi a wajen samun kuxin aiwatar da wannan shiri sun haxa da:

i- Tallafi daga gwamnatin tarayya, gwamnatin jiha, da kuma gwamnatocin qananan hukumomi.

 ii- Tallafi na musamman daga masu hannu-da-shuni.

iii- Tallafi daga qasashen qetare, musamman wasu qasashen Musulmi.

vi- Zakka da wakafi.

v- Neman sadaka musamman ta hanyar ajiye akwatuna a wuraren taruwar mutane kamar; Masallatai, kasuwanni, manyan shagunan da jamaa ke hada-hada a ciki, tashoshin mota, gidajen mai, maaikatun gwamnati, masu zaman kansu, makarantun islamiyya da na boko da sauransu.
 Duk kuxaxen da aka tara da su ne za a tallafa wa musakan da ke gidajen gajiyayyu, har ma da waxanda ke wajen danginsu da waxanda suke koyon sanaa da masu makarantun Al-Qurani.

4.2 Hukumar Gudanarwa
 Domin wannan shiri ya biya buqatar da ake so, dole ne a samar da wata qaqqarfar hukuma ko majalisa wadda za a xora wa alhakin samarwa tare da tattara kuxaxe, da kuma aiwatar da duk abin da ya kamata dangane da wannan shiri. Ya kamata wannan hukuma ta qunshi malamai da wakilan gwamnati da wakilan masarautu da kuma wakilan alumma daga kowane vangare.
Har wa yau kuma,  ya kamata wannan hukuma ta sami tsarin shugabanci mai kyau kamar; shugaba, mataimakin shugaba, sakataren kuxi, sakataren gudanarwa, maajin kudi, mai kula da shige da ficen kuxi, jamiin hulxa da jamaa, sauran mambobi da kuma babban sakatare.  Haka kuma, yana da kyau a sami wanzuwar wasu rassa na wannan hukuma masu wakilci a babbar hukuma ta kasa, da sauran jihohi da kuma matakan qananan hukumomi domin sauqaqe ayyukan hukumar.

5.0 Kammalawa
Sanin kowa ne cewa, a Arewacin qasar nan alummarmu ta Hausa-fulani su ne suka fi kowace alumma yawan mabarata a fadin wannan qasa tamu ta Najeriya.  Domin kuwa idan muka dubi alummar kudancin qasar nan ta fuskar kwatanci, za mu ga irin wannan matsala ta qaura a tsakaninsu a sakamakon matakai na taimakon juna da suka xora wa kansu da kuma kishin alummarsu.  Wannan dalili na matsalar bara ya sa ake yi wa wannan yanki namu kallon matalauta sun fi yawa, sannan kuma ana yi wa yanuwanmu wulaqanci da kallon qasqanci musamman a  yankunan kudu.
Idan muka yi nazari za mu ga yanzu idan yawan makafinmu dubu dari ne (100,000), to ya zama tilas yawansu ya ninka wanda muke da shi zuwa dubu dari biyu (200,000). Dalili kuwa shi ne, kowane makaho yana da xan jagora don haka su ma sun zama makafi, kuma zamu ga cewa mawuyacin abu ne waxannan yara su sami damar zuwa makarantar addini domin su san yadda za su aiwatar da ibada.  Har wa yau, akwai tausayi matuqa ta vangaren waxannan yara saboda ba su sami damar halartar makaranatar zamani ba, saboda da haka sai a ga sun girma amma rayuwarsu ta bambanta da ta sauaran jamaa saboda  yanayin rayuwar da suka tashi a ciki.  Haka nan kuma, matuqar aka xauki mataki yadda ya kamata, to muna kyatata zaton cewa wannan alumma tamu za ta yi bankwana da yin bara.  Bugu da qari kuma, yin hakan zai haifar da gagarumin ci gaba mai xorewa a cikin alummar  Musulmi da Hausa-fulani ‘yan asalin Arewa.

A dunqule, idan kuma muka lura da jerangiyar bayanan da suka gabata za mu iya cewa, matuqar aka xauki matakan da suka dace to za a iya daina bara a wani qanqanin lokaci kuma a ci gaba da yin almajirci.  A karshe zanso in ida rufe wannan rubutu nawa da wasu baitocin da Malam Saadu Zungur ya yi a cikin wakarsa ta Arewa Jamhuriya ko Mulukiya inda yake cewa :

Matuqar a Arewa da karuwai,
Wallahi za mu ji kunyar duniya.
Matuqar yan iska na gari,
 Dan daudu da shi da magajiya.
Da samari masu ruwan kuxi,
Ga maroqa can a gidan giya.
Babu shakka yan kudu za su hau,
Dokin mulkin Nijeriya.
Su yi ta kan sukuwa bisa kanmu ko,
Mun roqi zumuntar duniya.
Matuqar yaranmu suna bara,
Allah ba ku mu samu abin miya,
A gidan birni da na qauyuka,
Da cikin makarantun tsangaya.
Sun yafu da fatar bunsuru,
Babu shakka sai munsha wuya.
Matuqar da musakai barkatai,
Da makaho ko da makauniya.
Ba mahalli nasu a Hausa duk,
Babu mai tanyonsu da dukiya.
Birni qauye da garuruwa,
Duk suna yawo a garuruwa.
Kai Bahaushe ba shi da zuciya,
Za ya sha kunya nan duniya.
A Arewa zumunta ta mutu,
Sai nishaxi sai sharholiya.
Sai alfahari da yawan kwafe,
Girman kai sai kwamon tsiya.
Camfe-camfe da tsibbace-tsibbacen,
Malaman qarya yan duniya.
Cin amana kuma da yawan riya,
Ga hula mai annakiya.
Babu mai aiki bisa hankali,
Da basira don ya ga gaskiya.
Rantse-rantse da Allah ya yi yawa,
Ga qarya ga zambar tsiya.
Gorin asali dana dukiya,
Sai ka ce dan Annabi fariya.
Sai kinibibi sai kwarmato,
Ga gulma da son qullalliya.
Wagga alumma me za ta wo,
 A cikin zarafofin duniya.


©Mus'ab Nuraddeen Katsina (Mus'abulkhair)
musabnurakatsina@gmail.com
@musabulkhair_ktn

ALMAJIRCI DA BARA A MAHANGAR ILIMI

CASHLESS - A TAKAICE

22/09/2019 CASHLESS - A TAKAICE Cashless Policy - Wata doka ce da aka kirkiro domin a takaita mu'amala da tsuran kudi a wajen hada-...